AN GUDANAR DA JANA'IZAR SHADIN ABUJA SHAHID AHMAD RUFA'I A YAU TALATA A JANNATU DARURAHAMA

AN GUDANAR DA JANA'IZAR SHADIN ABUJA SHAHID AHMAD RUFA'I A YAU TALATA A JANNATU DARURAHAMA

A safiyar yau talata 24/04/2018 ne aka gudanar da Jana'izar Shidin Abuja wato Shahid Ahmad Rufa'i a Darur Rahama dake dambo a garin Zaria, Shahid Ahmad Rufa'i yayi shahada ne sakamakon harbin da yan sandan Nigeria suka masa a garin Abuja wajen Muzaharar Neman a saki Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria wato Sayyid Zakzaky {H}

An harbe shine a kansa a ranar litini 16/04/2018, ranar alhamis kuma Allah ya amsa abinsa, a safiyar yau talata kuma aka rufe sa a makwancin shahidai wato Darur Rahama, bayan an rufe shine Sheikh Abdulhamid Bello ya tunatar da yan uwa, matsayin shahada da kuma darajar shahidai , yayi kira kuma ga yan uwa da su dake a wannan Harkar kamar yanda Shahidan mu suka dake har suka samu rabo.

bayan ya kammala ne akayi addu'oi aka sallami Mutane

shahid

shahid

shahid

shahid


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky