An Gabatar da Shawarwari 7 Domin Fuskantar Kudurin Trump A Kan Qudus

An Gabatar da Shawarwari 7 Domin Fuskantar  Kudurin Trump A Kan  Qudus

Shugaban Jamhuriyar musulinci ta Iran Dakta Hassan Rauhani ya gabatarwa duniyar musulmi shawarwari guda bakwai domin kalubalantar kudurin shugaba Trump na Amurka a game da birnin Qudus, inda ya ce Amurka tana kare manufofin sahayuna ne ba tare da yin la'akari da na al'ummar Palastinu ba.

A yayin da ya gabatar da jawabinsa a taron gaggawa na shugabannin Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da ya gudana wannan laraba a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, shugaban jumhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya bukaci taron yayi alawadai da kudirin Amurka na bayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin HK Isra'ila, a matsayin shawara ta farko, sai shawara ta biyu, inda shugaba Rauhani ya bukaci dukkanin kasashen musulmi su hade wure guda domin kalubalantar wannan matsayi da Amurka ta dauka game da birnin Qudus.

Na uku, Shugaba Rauhani ya ce wajibi Amurka ta san cewa Duniyar musulinci ba za tayi wasa da makomar al'ummar Palastinu da Qudus ba, kuma ta san cewa izgilanci da tayi a game kudirin kasa da kasa kan  Palastinu,dole ne ta fuskanci martani mai karfi a siyasance, na huku kuma kamata yayi kasashen musulmi su tsaya tsayin daka wajen kalubalantar wannan kuduri ta hanyar tattaunawa da kawayen Amurka musaman kasashen Turai domin tilasta mata ta dawo daga wannan mataki. na biyar kuma Rauhani ya ce kamata yayi Duniyar musulimi ta sanya matsalar Palastinu a matsayin matsalar duniya ta farko da ya kamata a magance, bayan karya lagon 'yan ta'addar Da'esh a kasashenn siriya da Iraki.

A matsayin shawara ta shida da ta bakwai, shugaba Rauhani ya bukaci wakilan kasashen musulmi a zauren MDD da kwamitin tsaron MDD su hade wuri guda wajen kara kaimi na matsin lamba domin ganin an magance wannan matsala da kuma tilastawa Amurka na ta janye wannan kuskure da tayi, domin a halin da ake cikin zauren MDD da kwamitin tsaro gami da kungiyoyin kasa da kasa su ne za su taka mahimiyar rawa wajen bayyanawa Amurka adawarsu da wannan mataki da ta dauka a game da Qudus kuma ta janye shi cikin gaggawa.

A karshe Shugaba Rauhani ya ce Iran a shirye take ta hada kai da dukkanin kasashen musulmi da kuma bayar da dukkanin taimakon da ya dace domin kare birnin Qudus, sannan ya tabbatar da cewa musulmi da larabawa ba makiyan yahudawa ba ne, saidai suna adawa da shirin sahayuna mai cike da hadari ne.

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky