An Gabatar Da Muzaharar Lumana A Abuja

An Gabatar Da Muzaharar Lumana A Abuja

A jiya laraba ne, matasa karkashin dandamalin daliban harkar musulunci na Nigeriya suka gudanar da muzaharan lumana a garin Abuja, domin neman gwamnatin Nigeriya ta bi umurnin kotu ta saki jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda yake a tsare a hannun DSS tun Disambar 2015 duk da babban kotun tarayya tayi umurni da sake shi a watan Disambar 2016.
In ba a manta ba sojoji a lokacin da suka kai wannan hari a gidan Sheikh Zakzaky dake Zariya sun harbi malamin a wurare da dama na jikinshi wanda yayi sanadin rasa idonsa daya.Sannan an kashe masa 'ya'ya uku tare da harbin mai dakinsa a qugu.
Wadannan matasa dalibai sun gudanar da wannan muzaharan cikin tsari,suna dauke da kwalaye an rubuta free zakzaky, suna wake na neman a saki jagoransu,suna tafiya har zuwa inda zasu kulle muzaharan,kawai sa 'yan sanda suka zo suka fara antaya masu tiyagas.
Har zuwa lokacin hada wannan labarin bamu da labarin kama wani daga cikin masu muzaharan ko samun rauni daga cikinsu.
Kuna iya ganin wasu hotunan muzaharan a kasa:

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni