An fara taron tunawa da munasabar haihuwan Imam Ali Ar-Rida a Kano

An fara taron tunawa da munasabar haihuwan Imam Ali Ar-Rida a Kano

Yau Alhamis,3 ga watan Agusta 2017,Harkar Musulunci a Nigeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky ta fara gabatar da jerin tarukan da ta shirya domin tunawa da ranar haihuwan Imam Rida a Kano,wanda Ad-Da’iral Ammah ta saba shirya a duk shekara a Hussainiyyar Baqiyyatullah Zariya kafin a rusa ta.
A wannan shekarar taron an fara yinsa ne a Markaz dake Kofar Waika Kano tarayya Nigeriya,kuma za a kammala taron ranar Asabar mai zuwa.
Duk shekara akan canja tutar haramin Imam Ridha (as) da wata,wadda aka cire din ana kyautar da ita ga wani daga cikin masu hidima ga AhlulBait a duniya.To,a wannan shekarar an aikowa da Sheikh Zakzaky ita wannan tutan da aka cire a matsayin kyauta da karramawa.Bayan tutan ta isa ga Sheikh Zakzaky a in da yake a tsare.Sai Sheikh yayi umurni da baiwa Malam Sanusi Abdulkadir a matsayin girmamawa saboda sadaukarwansa,sannan kuma ya shirya taro na musamman dangane da Imam Ridha,sannan a sanya tutan a Hussainiyyar Markaz dake Kofar Waika.
Daga cikin abubuwan da aka gudanar yau a matsayin rana ta farko daga cikin jerin kwanaki uku na taron,bayan bude taro da addu’a da karatun Alkur’ani da karatun Ziyara,an gabatar da jawabai masu muhimmanci a wajen taron.
Sheikh Adamu Tsoho Jos a matsayin babban bako mai gabatar da kasida a wannan rana ya fara jawabinsa da taya ‘yan uwa murna na zagayowar wannan rana ta haihuwan Imam Ridha wanda bisa ludufin Allah ranar haihuwarsa ya zo daidai da ranar haihuwar ‘yar uwarsa Sayyidah Ma’asumah.
Shehun Malamin ya bayyana cewa “dole mu godewa Allah na samun kanmu cikin masu raya al’amarin AhlulBait.Na farko,mu godewa iyayenmu da ba a same mu ba ta hanyar da ba ta dace ba,kuma mu ba munafukai bane kaman yanda ta tabbata a riwaya.
“Ya zo a hadisi daga Imam Sadiq yana cewa Allah yayi rahama ga wanda ya raya al’amuran mu.Wannan irin taro namu yana daga cikin raya al’amarin AhlulBait.”
Shi kuma Sheikh Sanusi AbdulKadir a na shi jawabin bayan ya godewa Allah bisa ga wannan karramawa da Sheikh Zakzaky yayi masu ba wai don ya isa bane,ya bayyana cewa:
“Tutar Haramin Imam Ridha babu wadanda suke cirota sai mutum 4 a Iran,Sayyid Khamnae da wasu ne suke ciro ta.Bayan an ciro ta ana baiwa Sayyid Khamnae ya dauki tsawon lokaci yana tawassali da ita.Sannan ya dawo da ita yace a samu wani bawan Allah a duniya wanda yake yiwa addini hidima a bashi ita.
“Shine sai aka aiko ta ga jagoranmu Sayyid Zakzaky.Shima ya dauki lokaci yana tawassali da ita a inda yake tsare yanzu,sannan kuma ya aiko da ita nan Kano yace a shirya gaggarumin taro.Sayyid yace ya so a ce yana nan ya shirya taron da yafi na baya amma yanzu Dr Sanusi yayi iya kokarinsa ya ga taron anyi.”
Taron ya samu halartan ‘yan uwa maza da mata daga wurare daban daban cikin Nigeriya.Kuma taron yana gudana cikin nasara da taimakon Allah.

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni