An Dakile Wani Harin Ta'addanci A Kudancin Kasar Iran

An Dakile Wani  Harin Ta'addanci A Kudancin Kasar Iran

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun sanar da samun nasarar dakile wani harin ta'addanci da wasu 'yan ta'adda suka so kai wa lardin Sistan wa Baluchestan da ke Kudu Maso Gabashin kasar ta Iran

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran (IRNA) ya bayyana cewar a wata sanarwar da sashin hulda jama'a na sojin kasa na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya fitar ya ce a daren jiya Lahadi ne wasu gungun 'yan ta'adda cikin wata mota da suka makare ta da makamai da bama-bamai suka yi kokarin kai wani harin kunar bakin wake ga daya daga cikin sansanin sojin kasa na dakarun da ke yankin Saravan na lardin Sistan wa Baluchestan, to sai dai dakarun sun sami nasarar dakile wannan harin.

Sanarwar ta kasar da cewa dakarun kare juyin sun sami nasarar hallaka 'yan ta'adda guda biyu daya kuma ya tarwatsa kansa inda ya halaka, sai dai wasu dakarun sa kai na Iran (Basij) su biyu sun sami raunuka.

Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai 'yan ta'addan, wadanda suke shigowa daga kasar Pakistan, sun sha kokarin kai hare-hare ga dakarun kan iyaka na Iran a yankuna kan iyaka da suke lardin na Sistan wa Baluchestan, lamarin da ke fuskantar turjiya daga wajen dakarun na Iran, duk kuwa an sami wasu daga cikin dakarun da suka yi shahada


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky