An Dage Sauraren Shari'ar Sheikh Zakzaky Har Zuwa 2 Ga Watan Agusta

An Dage Sauraren Shari'ar Sheikh Zakzaky Har Zuwa 2 Ga Watan Agusta

Rahotanni daga Najeriya sun ce Kotun da ke sauraren shari'ar sheikh Ibrahim Zakzaky ta sanar da dage sauraren shari'ar har zuwa ranar 2 ga watan Agusta mai kamawa.

Kotun da ke da mazauni a garin Kaduna da ke arewacin Najeriya, ta sanar da cewa ta dage zaman shari'ar wanda ya kamata a gudanar a yau, sakamakon rashin halartar biyu daga cikin wadanda ake tuhuma tare da sheikh Zakzaky.

Gwamnatin Jahar Kaduna karkashin gwamna Nasir Elrufai tana zargin sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa malaman Zinat Ibrahim tare da sheikh Yakubu Yahya da kuma Malam Sanusi Abdulkadir da kisan soja guda, a  lokacin farmakin da sojoji suka kaddamar kan gidan sheikh Zakzakya  Gyallesu a karshen 2015, inda lauyan gwamnatin ta Kaduna ya tabbatar da cewa an bizne gawawwakin mabiya sheikh Zakzaky 347 da sojoji suka kashe a lokacin, yayin da mabiya harkar musulunci suka ce mutanen da sojoji suka kashe a lokacin sun kai mutane 1000, tare da fitar da jerin sunayensu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky