An Bukaci Da A janye kariyar Ga wadanda suka kashe Khashoggi"

An Bukaci Da A janye kariyar Ga wadanda suka kashe Khashoggi

Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci janye rigar kariya ta hukumomin da ke da hannu a bacewar dan jaridan Saudiya, Jamal Khashoggi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, shugabar hukumar, Michelle Bachelet ta bayyana cewa, akwai bukakar janye rigar kariyar lura da girmar al’amarin da ke tattare da bacewar Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiya a Turkiya.

Duk da cewa, akwai yarjejeniyar Vienna ta 1963 da ke kare hurumin ofisoshin jakadancin kasashen duniya, amma Hukumar Kare Hakkin Bil’adaman na bukatar daukan matakin janye kariyar wadanda ke da hannu a bacewar .

Tuni Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya isa birnin Riyadh na Saudiya don tattaunawa da Sarki Salman kan bacewar dan jaridan.

Tun a ranar 2 ga watan Oktoba ne Khashoggi ya bacewa bayan tabbatar da shigarsa ofishin jakadancin Saudiya a birnin Santanbul na Turkiya, yayin da ake zargin hukumomin Saudiya da kitsa kashe shi saboda yadda yake sukar manufofin gwamnatin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky