An Bukaci A Rage Cinkoso A Gidajen Yarin Nageria

An Bukaci A Rage Cinkoso A Gidajen Yarin Nageria

Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) a tarayyar Najeriya ta bukaci gwamnonin kasar su dauki mataki kan fursinonin da aka yankewa hukuncin kisa a jihohinsu don sun zama barazana ga tsarin gidajen yari a kasar

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa majalosar ta NEC ta gudanar da taro a fadar shugaban kasa a ranar Laraba inda Ministan sharia kuma Anthony janar na kasar Abubakar Malami ya gabatarwa majalisar maganar fursinoni 2359 wadanda aka riga aka yanke masu hukuncin kisa, amma kuma ake ci gaba da tsaresu ba tare da an zartar da hukuncin da aka yanke masu ba.

Malami ya bukaci gwamnomin jihohin kasar 36 da su aiwatar da hukuncin da aka yakewa wadannan fursinoni ko kuma su sake shari'arsu kamar yadda doka ta 212 ta amince masu. don a rage cinkoso a gidajen yarin kasar.

Amma gwamnan jihar Bauchi Mohammad Abdullahi Abubakar ya bayyana wa Daily Trust cewa akwai matsaloli tattare da aiwatar da irin wannan hukuncin, don misali babu kayakin aikin aiwatar da hukuncin kisa a Bauchi amma idan an kai fursininin jos a cikin shardan yin haka sai gwamnann jihar Plato ya sanya hannu kan takardunn kisan kafin a aiwatar da shi wanda a mafi yawan lokuta ba sa amincewa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky