An Bukaci A Kwace Lambar Nobel Da Aka Bai Wa firayi minstar kasar Myanmar

An Bukaci A Kwace Lambar Nobel Da Aka Bai Wa firayi minstar kasar Myanmar

Kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta bukaci da kwace lambar nobel ta zaman lafiya da aka bai wa firayi minstar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi da aka ba ta a cikin 1991.

Shafin yada labarai na freepen ya bayar da rahoton cewa, kungiyar ta ISESCO ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar daga babban ofishinta da ke birnin Rabat na kasar Morocco.

A cikin bayanin kungiyar ta bayyana cewa, mutanen irin su Aung San Suu Kyi ba su cancanci samun lambar yabo ta zaman lafiya ta nobel ba, idan aka dubi irin kisan kiyashin da gwamnatinta take yi wa musulmi a kasar Myanmar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, kisan kiyashin da ake yi wa musulmi a halin yanzu haka  akasar Myanmar, lamari ne da ya cancanci dukkanin kasashen duniya su dauki matakin ladabtarwa a kan gwanatin kasar Myanmar a kansa, sakamakon kisan dubban muusulmi 'yan kabilar Rohingya a cikin kasa da mako guda.

Haka nan kuma bayanin ya bukaci da a gurfanar da Aung San Suu Kyi a gaban kotun manyan laifuka ta duniya domin ta fuskanci hukunci.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky