An Bude Shirin Kera Makamai Masu Limzami Samfurin Fakur Anan Kasar Iran

An Bude Shirin Kera Makamai Masu Limzami Samfurin Fakur Anan Kasar Iran

A jiya litinin ne ministan tsaron kasar Iran ya bude shirin kera makamai masu linzami mai suna Fakur a nan kasar don amfani da su a jiragen yakin kasar a duk lokacin da bukatar haka ta taso.

Muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto  Brigadier Amir Hatami ministan harkokin tsaron kasar Iran yana cewa a cikin watan Afrilun shekara ta 2017 ne masana a cikin gida suka tsara, suka kera sannan suka gwada makamin mai linzami na Fakur tare da samun nasara. 

Ministan ya kara da cewa a halin yanzu za'a fara kera wadannan makamai gwagwardon bukata sojojin samar kasar. Ya ce Fakur wani makami mai linzami ne mai amfani da rada kuma aka kera shi da fasahar zamani don amfani da shi a jiragen saman yakin kasar. 

Daga karshe ministan ya kammala da cewa kasar Iran zata ci gaba da samarda makaman da sojojin kasar suke bukata don tabbatar da tsaron kasar. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky