An Bude Hanyar Maiduguri-Bama-Banki Dake Hannun B/Haram Na Tsawon Shekaru

An Bude Hanyar Maiduguri-Bama-Banki Dake Hannun B/Haram Na Tsawon Shekaru

Sojojin Nijeriya sun gudanar da bikin bude hanyar Maiduguri-Bama-Banki da ke jihar Borno a yau din nan Asabar shekaru hudu bayan da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram suka kwace hanyar, lamarin da mutanen yankin suka yi maraba da shi

Kafar watsa labaran Premium Times ta Nijeriya din ta ce tun da safiyar yau ne dai sama da kananan motoci, manyan motocin daukar kaya da sauransu 100 ne cike da fasinjoji da kayayyaki suke sahu a kan babban titin Maiduguri-Bama din suna jiran sojojin su sanar da bude hanyar wacce a baya ta zamanto daya daga cikin hanyoyi mafiya hatsari a jihar.

Yayin da yake sanar da bude hanyar, Kwamandan Operation Lafiya Dole, don fada da Boko Haram din Manjo Janar Nicholas Rogers, ya ce dakarun nasa sun yi gagarumin aiki wajen rage irin kaifin ayyukan 'yan ta'addan na Boko Haram a yankin, yana mai cewa dakarun nasa za su ci gaba da iyakacin kokarinsu wajen tabbatar da tsaron hanyar da kuma kawar da nakiyoyin da mai yiyuwa 'yan ta'addan sun bisne su, don haka ya kirayi jama'a da cewa aikin sojojin zai yi nasara ne kawai a yayin da suke ba su hadin kai da kuma bin dokokin da aka tsara musu.

Duk da irin damuwar da wasu suke da ita dangane da tabbatar da tsaron hanyar mai tsawon kilomita 75, to amma mutanen yankin sun nuna farin cikinsu da sake bude hanyar wacce aka rufe ta a watan Satumban 2014 saboda hare-haren 'yan kungiyar ta Boko Haram.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky