An Bayyana Wasu Daga Cikin Matakan Da Saudia Da Kawayenta Zasu Dauka A Kan Qatar

An Bayyana Wasu Daga Cikin Matakan Da Saudia Da Kawayenta Zasu Dauka A Kan Qatar

Wani dan majalisar dokokin kasar Masar Ya bayyana wasu matakan da kasashe hudu wadanda suka dorawa kasar Qatar takunkumai zasu dauka bayan rashin gamsuwarsu da amsar da ta bayar kan sharuddansu na farko

Majiyar muryar jumhriyar musulunci ta Iran daga birnin Alkahira ta nakalto Mohammad Maahir Haamid, wani dan majalisar dokokin kasar bayan yana bayyana wasu matakan da kasashen Saudia, Bahrain Emirate da kuma Masar zasu dauka a kan kasar Qatar bayan rashin gamsuwarsu da amsar da Qatar din ta bayar kan sharuddansu guda 13 na sake dawo da hulda a tsakaninsu da ita.

Haamin ya ce, matakan sun hada da jingine kasar Qasar daga zama memba a kungiyar kasashen larabawa na yakin tekun Farisa, da kuma na kungiyar kasashen Larabawa, tsaida harkokin kasuwanci da kasar, sannan tare da ingiza manya manyan kasashen duniya su kauracewa Qatar a harkokin kasuwanci.

Dan majalisar ya kara da cewa wannan kadanne daga cikin mataki na gaba wadanda wadan nan kasashe hudu zasu dauka a kan kasar Qatar nan ba da dadewa ba. 

A ranar 5-Yunin da ya gabata ne kasashen Qatar, Bahrai, Saudia da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka katse huldar diblomasia da kasar Qatar tare da zarginta da goyon bayan yan ta'adda da msu wuce gona da iri a cikin addini.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky