Amurka Ta Soke Visar 'Yan Saudiyya da Ake Zargi Da Kashe Kashoggi

Amurka Ta Soke Visar 'Yan Saudiyya da Ake Zargi Da Kashe Kashoggi

Amurka ta sanar da wani matakinta na soke takardar iznin shiga kasar watau visa, ga 'yan Saudiyya da suke da hannu a kisan gillan da aka wa dan jaridan nan Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Santanbul yau da kusan mako uku.

Da yake sanar da matakin ga manema labarai sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce tuni gwamnatin ta Washigton ta gano wasu mutane dake da hannu a kisan dan jaridan.

Koda yake Mista Pompeo bai fayyace adadinsu ba, amma ya ce mutanen sun hada da jami'an leken asirin masarautar da kuma na ma'aikatar harkokin wajen Saudiyyar.

Ministan harkokin wajen Amurka ya kara da cewa, akwai yiyuwar kuma a takaita tafiya tafiyen masu zargin da kuma toshe kaddarorinsu a cikin Amurka.

Wannan dai na zuwa ne bayan bayyanin da shugaba Recep Tayeb Erdogan na Turkiyya ya yi a jiya cewa '' Saudiyya ta kwashe kwanaki da dama tana shirya yadda za'a kashe dan jaridan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky