Amurka Ta Bukaci Komitin Tsaro Na MDD Ta Dorawa Kasar Iran Takunkumi

Amurka Ta Bukaci Komitin Tsaro Na MDD Ta Dorawa Kasar Iran Takunkumi

Mataimakin jakadan Amurka a majalisar dinkin Duniya Jonathan Cohen ya bukaci komitin tsaro na MDD ya dorawa JMI takunkumai don abinda ya kira sharrin Iran a yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto jonathan yana cewa kasar Iran ce take bawa mayakan Huthi na kasar Yemen makamai masu linzamin da suke cillawa kan kasar Saudia. Don haka a fadinsa Iran ta sabawa dokokin kasa da kasa na hana bawa yan ta'adda irin wadan nan makamai.

Jonatahan Cohen ya na wannan magana ce a lokacinda majalisar da kuma komitin tsaron suka dage kan cewa babu wata hujja wacce ta tabbatar da ikrarin na Amurka.

Hakama dangane da shirin Iran na makamashin Nukliya hukumar IAEA ta fitar da rahoto na goma a ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata kan cewa kasar Iran tana ci gaba da mutunta yerjejniyar Nucliyar kasar.

Banda haka Amurkan ta kira sauran kasashen duniya da su kauracewa Iran saboda wadannan dalilai, amma ba bu wata kasa  da ta amsa kiran har yanzun.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky