Amruka Na Zargin Cewa Mai Yiyuwa Kashe Kashoggi Akayi

Amruka Na Zargin Cewa Mai Yiyuwa Kashe Kashoggi Akayi

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce mai yiyuwa ne an kashe dan jaridan nan ne na Saudiyya Jamal Khashoggi.

Trump ya bayyana hakan ne ga 'yan jarida bayan wata hira ta wayar tarho da sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz  kan batun dan jaridan da ya bace yau sama da mako biyu.

Saidai sarkin Saudiyyar ya ce kasarsa ba tada wata masaniyya dangane da batun dan jaridan Jamal Khashoggi. 

Shugaba Trump ya ce ya aike da sakataren harkokin wajensa Mike Ponpeo zuwa Saudiyyar domin ci gaba da tattauna wannan batu da sarkin Saudiyyar.

A wani labari yau Litini ce ake sa ran za'a gudanar da bincike a cikin karamin ofishin jakadancin na Saudiyya dake birnin Santanbul inda nan ne dai dan jaridan ya bace tun bayan shigarsa ofishin a ranar 2 ga watan Oktoba.

Jami'an tsaron Turkiyya dai sunyi amanar cewa an kashe dan jaridan ne a cikin ofishin, batun da Saudiyya ke ci gaba da musuntawa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky