Amnesty Int. Ta Yi Kakkausar Suka A Kan Gwamnatin Saudiya Kan Kisan Fararen Hula

Amnesty Int. Ta Yi Kakkausar Suka A Kan Gwamnatin Saudiya Kan Kisan Fararen Hula

Kungiyar Amnesty Internatinal ta yi kakkausar a kan masarautar 'ya'yan Saud da ke rike da madafun iko a kasar Saudiyya, dangane da kisan fararen hula masu nuna adawa da salon mulkinsu.

A cikin bayanin da kungiyar ta fitar a jiya, ta bayyana cewa masarautar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa har lahira  akan wasu fararen hula guda 4 da take tsare da su, dukkaninsu 'yan yankin Qatif ne na mabiya mazhabar shi'a da ke gabashin kasar, bisa tuhumarsu da ayyukan ta'addanci.

Kungiyar Amnesty Int. ta ce bisa ga bincikenta babban laifin da wadannan mutane suka aikata ga gwamnatin Saudiyya shi ne, sun shiga cikin zanga-zangar nuna adawa da salon mulkin kasar ne da suke ganin yana tauye musu hakkokinsua  matsayinsu na 'yan kasa,a  kan haka gwamnatin Saudiyya ta harbe su a ranar Talata da ta gabata.

Al'ummar yankunan gabashin saudiyya wadanda mabiya mazhabar shi'a ne, suna kokawa dangane da yadda aka mayar da su saniyar ware da kuma haramta musu dukkanin hakkokinsu na 'yan kasa a kasarsu, tare da cewa dukkanin arzikin man fetur da iskar gas da tattalin arzikin kasar ya dogara a kansa, daga yankunansu ake hako su.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky