Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun gudanar da muzaharori domin nuna Allah wadai da watsi da karar Sheikh Zakzaky da Babban kot

Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun gudanar da muzaharori domin nuna Allah wadai da watsi da karar Sheikh Zakzaky da Babban kot

A ranar Alhamis din da ta gabata ne,Alkalin babban kotun tarayya na Kaduna yayi fatali da karar da babban malamin Shi’a a Nigeriya wato Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar domin neman haqqoqinsa da aka tauye.
Tun bayan wannan hukunci na wannan Alkali ‘yan uwa da masoya wannan malami suke ta nuna alhinin su dangane da wannan hukunci na wannan Alkali.
A jiya juma’a,’yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky a wurare da dama a fadin Nigeriya sun gudanar da muzaharori na nuna rashin amintarsu da jin dadin su da wannan hukunci na babban kotun tarayya ta Kaduna.
Malam Hasan Adam,wakilin ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky na garin Suleja a lokacin da yake jawabi bayan kammala muzaharan a garin Suleja ta jihar Nigeriya,ya nuna takaicinsa dangane da irin ta’addancin da aka yiwa Sheikh Zakzaky na rusa masa gida da kashe masa almajirai wadanda suka hada da ‘ya’yan cikinsa da kuma harbin malamin a wurare da dama na jikinsa da kuma cigaba da tsare shi ba akan wani dalili ba.
A garin Kano ma anyi irin wannan muzahara,inda Malam Sanusi AbdulKadir ya jagorance ta.An fara wannan muzaharan ne daga kofar masallacin juma’a na Fagge aka biyo ta Ibrahim Taiwo,sannan aka kammala a randan Sheikh Isyaka Rabi’u.
Malam Sanusi Abdulkadir a lokacin jawabin kammala muzaharan yayi kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin Sheikh Ibrahim Zakzaky ba tare da wani sharadi ba.Sannan kuma ta mutunta doka ta biya shi diyya.
A karshe yayi kira da ‘yan uwa ka da su gajiya wajen fafatikan ganin an sako Sheikh Ibrahim Zakzaky

Nageria

Nageria

Nageria

Nageria

Nageria


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky