Alkalin Babban kotun Tarayya na Kaduna ya kori karar da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar yana neman hakkokinsa.

Alkalin Babban kotun Tarayya na Kaduna ya kori karar da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar yana neman hakkokinsa.

A yau ne Alkalin babban kotun tarayya dake Kaduna ya yanke hukuncidangane da karar da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar a wannan kotu.In ba a manta ba Sheikh yayi karar rundunar sojan Nigeriya,da Antoni Janar na tarayya,da kuma gwamnatin jihar Kaduna domin neman hakkokinsa da aka tauye.
Alkalin kafin yanke wannan hukunci,sai da ya karanto dalilin shigar da karar da dukkan tattaunawar da lauyoyi suka yi a lokacin sauraron karar a baya.Daga cikin abubuwan da alkalin ya fadi yace :
“Sheikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddeen Ibrahim sun nemi kotu da tayi masu adalci,saboda wanda suke kara na farko(soja) da na biyu sun je gidansu a Gyellesu dake Zariya Kaduna suka hallaka musu ‘ya’ya uku tare da kona musu gida da kuma harbinsu da tsare su tare da umurnin kotu ba,wanda wannan ya saba ma dokokin ‘yancin dan Adam.
“Sannan suna neman a hana dukkan wadanda suke takura musu takura masu,sannan a biya su diyyan Naira biliyan biyu.”
Alkalin ya cigaba da cewa:
“Lauyan wanda ake kara na uku,ya bayyana cewa shigar da kara guda biyu iri daya a kotu daban kuma ana neman abu guda raina kotu ne.
“Lauyan masu gabatar da kara ya bayyana cewa shari’ar da aka yi a Abuja ba iri daya ba ce da ta wannan kotun na Kaduna.In da ya bayyana cewa a Abuja sun nemi da a saki Sheikh Zakzaky ne saboda a can ake tsare da shi ,a nan kuma suna magana ne akan rushe rushe da aka yi masu.”
Alkalin ya nuna bai yarda da wannan maganar da lauyoyi masu gabatar da kara suka yi ba.Sannan kuma Alkalin ya karanto takardar da Lauyan Sheikh Zakzaky,Chif Femi Falana (SAN) wanda a ciki yake cewa gwamnatin tarayya ta daukaka karan shari’ar Abuja,amma shi Alkalin yace wannan kotun ba ta da ikon binciken abinda ke kotun daukaka kara.
A karshe dai Alkalin ya kori wannan karar da dalilin cewa ba a bi hanyoyin da ya kamata a bi ba wajen shigar da karan.
Bayan an fito daga sauraran karar,’yan jaridu sun zanta da daya daga cikin lauyoyin da ke kare Sheikh Zakzaky wato Lauya Festus Okoyo domin jin albarkacin bakinshi, in da yake cewa:
“Kamar yadda a tsarin shari’a mai kara shine mai “case”,lauya wakilinsa ne.Mai kara shi zai yanke hukuncin abinda za a yi.Shi lauya na shi ya bada shawara.
“Don haka za a sanar da Sheikh Zakzaky wannan hukunci,shi kuma zai yanke abinda za a yi,ko a karbi hukuncin,ko a daukaka kara.Sai dai lauyoyi za su ba Sheikh shawara akan abinda suke ganin ya dace.

Kotu

Kotu

Kotu

Kotu

Kotu


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

asura-mystery-of-creation
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky