Alakar Iran Da EU, Zarif Ya Gana Da Mogherini

Alakar Iran Da EU, Zarif Ya Gana Da Mogherini

Muhammad Jawad zarif tare da babbar jami'ar siyasar wajen tarayyar turai Federica Mogherini sun gana a birnin Oslo na kasar Norway.

Ganawar bangarorin biyu dai ta gudana ne a daren jiya Litinin, inda suka tattauna a kan batun matakan da Amurka take dauka a kan Iran da suka yi hannun riga da yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Ministan harkokin wajen na Iran ya sheda wa Mogherini cewa, idan har Amurka ta ci gaba da daukar matakan da suba wa yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a kan shirinta, to shakka babu Iran za ta dauki matakin mayar da martanin da take ganin ya dace.

A nata bangaren Federica Mogherini ta bayyana cewa, kungiyar tarayyar tana mutunta yarjejeniyar da aka cimmawa tare da Iran, kuma za ta ci gaba kare wannan yarjejeniya.

A bangare guda kuma bangarorin biyu na Iran da kungiyar tarayyar turai sun tattauna batun rikicin Syria da Qatar da sauran kasashen larabawa, da kuma wajabcin shawo kan wadannan matsaloli ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna..288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni