Al-Qa'ida Ta Dauki Alhakin Kai Harin Birnin Ouagadougou

 Al-Qa'ida Ta Dauki Alhakin  Kai  Harin Birnin Ouagadougou

Wata kungiyar ta'addanci da ke da alaka da kungiyar Al-Qa'ida ta dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai birnin Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso a shekaran jiya Juma'a da yayi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin mutane 30, ciki kuwa har da maharan su takwas.

Kafar watsa labaran Alakhbar ta bayyana cewar kungiyar Jama’a Nusrat ul-Islam wa al-Muslimin (JNIM) da ke da helkwata a kasar Mali, cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya Asabar, ta dauki alhakin kai harin Birnin Ouagadougou inda ta ce ta kai harin ne a matsayin mayar da martani ga kashe daya daga cikin jagororin kungiyar,  Mohamed Hacen al-Ancari, da sojojin Faransa suka yi.

Tun a shekara ta 2013 ne dai kasar Faransa ta tura sojojinta kasar Mali din da nufin korar masu tsaurin ra'ayin addini da suka kwace wani yanki na arewacin kasar, har ya zuwa yanzu kuma tana da kimanin sojoji 4000 a yankin Sahel a matsayin wani bangare na ci gaba da fada da ta'addanci da ake yi.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai wasu mahara dauke da makamai da ababen fashewa suka kai wasu munanan hare hare ga helkwatar rundunar tsaron sojan kasar Burkina Fason da birnin Ouagadougou bugu da kari kan ofishin jakadancin Faransa da na wata cibiyar kasar Fransa lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 30 baya ga wadanda suka sami raunuka.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Prophet's birthday celebrations
We are All Zakzaky