Akalla Mutane 80 Sun Mutu, Wasu Daruruwa Sun Jikkata A Harin Ta'addanci A Afghanistan

Akalla Mutane 80 Sun Mutu, Wasu Daruruwa Sun Jikkata A Harin Ta'addanci A Afghanistan

Rahotanni daga kasar Afghanistan sun bayyana cewar alal akalla mutane 80 sun rasa rayukansu kana wasu daruruwa kuma sun sami raunuka sakamakon wani kazamin harin bam da aka kai yankin da ke dauke da ofisoshin jakadancin na kasashen waje a birnin Kabul babban birnin kasar ta Afghanistan.

Wani jami'in gwamnatin kasar Afghanistan din ya shaida wa manema labarai cewa harin ya faru ne da safiyar yau din nan Laraba inda aka tayar da bam din a wannan yanki mai matsanancin tsaro kusa da mashigar ofishin jakadancin kasar Jamus inda alal akalla mutane 80 suka musu wasu kuma kimanin 350 suka jikkata mafiya yawansu fararen hula ne 'yan kasar Afghanistan din.

Rahotannin sun ce tsananin karfin bam din da ya tashin ya sanya farfashewar tagogi da kofofin gine-ginen da ke da nisan daruruwan mitoci daga wajen da fashewar ta faru, har ila yau kuma gine-ginen ofisoshin jakadanci na kasashe da dama, ciki kuwa har da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun tabu da kuma lalacewa  sakamakon fashewar wannan abu mai karfin gaske.

Kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) ta ce ita ce ta kai wannan harin a ci gaba da irin hare-haren ta'addancin da ake kai wa kasar ta Afghanistan, wacce take a matsayin daya daga cikin kasashen da suke rashin tsaro a duniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky