Afrika ta Kudu ta kama jirgin ruwa makare da makamai da ya nufi Najeriya

Afrika ta Kudu ta kama jirgin ruwa makare da makamai da ya nufi Najeriya

Jami’an tsaro a Afirka ta Kudu sun sanar da kama wani jirgin ruwan kasar Rasha dauke da makamai da sauran abubuwa masu fashewa da aka ce yana kan hanyarsa ce ta zuwa tashar jiragen ruwan birnin Lagos a Najeriya.

Jirgin mai suna Lada, ya baro kasar Madagascar ne kafin ya isa tashar ruwan Port Elizabeth a Afirka ta Kudu, yayin da makaman da ke ciki aka kiyasta cewa kimarsu ta kai dalar Amurka milyan 3 da rabi.

An gano makaman ne boye a cikin kwantenoni 20, kamar dai yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar.

A cikin shekarun baya-bayan nan, sau da dama jami’an tsaron Najeriya na kama makamai da aka shiga da su cikin kasar ba a kan ka’ida ba.

Wata kididdiga da aka fitar a baya bayan nan kamar yadda jaridar The Nation da ake wallafa ta a Najeriya ta rawaito, ta nuna cewa tsakanin shekarun 2010 zuwa 2017 da ta gabata, an yi fasakaurin makamai hadi da alburusai, zuwa cikin Najeriya ta ruwa da yawansu ya kai miliyan 21 da dubu 500.

A watan Nuwamba na shekarar 2010, jami’an kwastam a Najeriya suka kama tarin makaman da yawansu ya kai dubu 21 da dari 407, a tashar jiragen ruwa da ke Apapa a garin Legas, yayinda kuma a watan Satumba na shekarar 2017, a tashar jiragen ruwa ta Tin-can duk da ke garin na Legas aka kame manyan bindigogi masu sarrafa kansu dubu 1 da guda 100, wadanda aka yunkurin yin fasakaurinsu zuwa cikin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky