Afganistan : An kai Hari A Masallacin 'Yan Shi'a

Afganistan : An kai Hari A Masallacin 'Yan Shi'a

Rahotanni daga Aganistan na cewa gomman mutane ne suka rasa rayukansu, a wasu jerin hare haren kunan bakin wake a wani masallacin Juma'a dake gabashin kasar

An dai kai harin ne a lokacin jama'a ke sallar Juma'a, inda maharan suka bude wuta kan masallatan, kafin daga bisani su tada boma boman da sukayi jigida dasu a cewar shugaban 'yan sanda yankin.

Wani likita a yankin na Gardez, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, an kai masu gawawakin mutane sama da 70, kuma adadin mutaten ma zai iya karuwa.

Kafin hakan kakakin gwaman Lardin, Abdullah Hasrat, ya ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 22, baya ga wasu 25 da suka raunana.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky