A Nijeriya An Zargi Dino Melaye Da Raba Makamai Don Tada Hankali

A Nijeriya An Zargi Dino Melaye Da Raba Makamai Don Tada Hankali

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gabatar da wasu matasa da ta kama bisa zargin suna da alaka da wata kungiyar ‘yan ta’adda da suke gudanar da ayyukansu a jihar Kogi wadanda suka ce dan majalisar dattawan Nijeriyan Sanata Dino Melaye ne ke ba su makamai

Kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya Moshood Jimoh ne ya bayyana hakan a lokacin da yake  nuna wa manema labarai wadannan matasa guda biyu, wato Kabiru Saidu da Nuru Salisu, a birnin  Lokoja, babban birnin jihar Kogin, inda rundunar ta dade ta na farautar mutanen har zuwa lokacin da dubunsu ya cika aka kama su da makamai ciki kuwa har da bindigogi samfurin AK-47.

Mr. Jimoh ya kara da cewar yayin gudanar da bincike mutanen biyu sun bayyana wa 'yan sandan cewa Sanata Dino Melaye ne ya ke ba su makamai da kuma kudade da suke gudanar da ayyukansu. Don haka ya ce a halin yanzu rundunar tana neman Sanata din don neman karin bayani daga bakinsu.

A kwanakin baya ma dai 'yan sandan sun yi kokarin kama Sanata Melaye a babbar kotun Abuja, to sai dai kuma ya samu ya gudu ba tare da sun kama shi ba.

Baya ga wannan batu har ila yau kuma Sanata Melayen yana fuskantar matsalar kiranye da mutanen mazabansa suka gabatar wa hukumar zaben Nijeriya suna masu cewa sun gaji da wakilcin da yake musu a majalisar dattawan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky