A Kashe Wasu 'Yan Ta'adda Biyu A Iran Inda Aka Kama Wasu Da Dama

A Kashe Wasu 'Yan Ta'adda Biyu A Iran Inda Aka Kama Wasu Da Dama

Jami'an tsaro a kasar Iran sun bada sanarwar kashe yan ta'adda biyu sun kuma kama wasu biyar a wani samame da suka kai a mabuyar yan ta'addan a yankin chabahar na jahar Sistan-Buluchistan a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Presstv da ke tehran ta jiyo ministan ayyukan leken asiri na kasar Mahmood Alavi ya na bayyana haka a jiya da yamma. Ya kuma kara da cewa an gano makamai da kuma boma boman kunan bakin wake da dama a hannunsu. Sai dai wani jami'in tsaron kasar guda ya yi shahada a arangamar da suka yi da yan ta'addan.

Alavi ya ce biyu daga cikin mutanen da aka kama 'ya'yan wata kasa she daga kasashe makobta. Banda haka ministan ya ce sun wargaza wani shiri na kai hare haren ta'addanci a kasar a yankin Kurdistan.

A wani labari kuma kamfanin dillancin labaran IRNA ya ce yan ta'addan da aka kashe ko aka kama a jiya Laraba 'ya'yan wata kungiyar yan ta'adda wacce ake kira Ansar al-furqan ne.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky