?>

Morocco Na Karbar Bakuncin Taron Duniya Kan Yaki Da Kungiyar IS

Morocco Na Karbar Bakuncin Taron Duniya Kan Yaki Da Kungiyar IS

A Maroko yau Laraba ne ake bude taron ministoci karo na 9 na kungiyar hadin gwiwa ta duniya kan yaki da kungiyar Daesh ko IS.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan taro, wanda Maroko da Amurka suka shirya, zai ba da "muhimmanci ga nahiyar Afirka", a cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Morocco ta fitar.

Kimanin tawagogi hamsin ne ake sa ran zasu halarci taron na Marakesh, ciki har da 15 daga Afrika.

Wannan shi ne karon farko da ake gudanar da wannan taro a nahiyar.

Daga cikin bakin na Afirka akwai kasashe da suka fito daga yammacin Afirka, kamar Burkina Faso, Nijar da Benin.

A shekarar 2014 ne aka kafa kungiyar ta yaki da kungiyar ta IS, wacce ta kunshi malalarta tamanin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*