?>

Morocco : Kungiyoyin Kwadago Sun Kira Yajin Aikin Gama-gari

Morocco : Kungiyoyin Kwadago Sun Kira Yajin Aikin Gama-gari

Kungiyoyin kwadago a Morocco, sun yi kiran shiga wani yajin aikin gama-gari a ma’aikatun gwamanti a gobe Litini a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Makasudin kiran yajin aikin shi ne nuna bacin rai game da matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar.

A sanarwar da manyan kungiyoyin kwadago na kasar guda uku suka fitar, sun kuma bukaci karin albashi ga ma’aiakata da kuma wadanda je ritaya, saboda tsadar rayuwa, mai nasaba da hauhawan farashin man fetur da kuma ababen bukatuwa na yau da kulun.

Sakatare janar na kungiyar kwadago ta ODT, yayin wani taron manema labarai ya bayyana yajin aikin da gargadi ga gwamnati akan ta dauki matakai akan hauhawan farashin na kayan abinci da kuma man fetur.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*