?>

Mohamed bin Zayed Al Nahyan, Ya Zama Sabon Shugaban UAE

Mohamed bin Zayed Al Nahyan, Ya Zama Sabon Shugaban UAE

Majalisar koli ta Tarayyar Hadaddiyar Daular Larabawa ta zabi Yarima mai jiran gado Mohamed bin Zayed Al Nahyan a matsayin shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tsohon Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu a ranar Juma'a, 13 ga Mayu, yana da shekaru 73 a duniya.

Khalifa bin Zayed shi ne babban dan Zayed bin Sultan Al Nahyan, wanda ya kafa gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma shi ne yarima mai jiran gadon sarauta, wanda ya mulki Abu Dhabi bayan rasuwar mahaifinsa.

Khalifa bin Zayed shi ne shugaban kasa na biyu na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa tun bayan kafuwarta a ranar 2 ga Disamba, 1971, kuma shi ne shugaban Abu Dhabi na 16.

Tuni shuwagabannin duniya suka fara aika masa da sakon taya shi murna, da kuma fatan ci gaba da yin aiki tare.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*