?>

MDD Ta Yi Kiran Samar Da Daidaito A Kokarin Kawo Karshen AIDS A 2030

MDD Ta Yi Kiran Samar Da Daidaito A Kokarin Kawo Karshen AIDS A 2030

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a yi kokarin kawo karshen rashin daidaito domin dawo da duniya kan turbar fatattakar yaki da cutar kanjamau nan da 2030.

ABNA24 : Antonio Guterres, ya ce an samu gaggarumar nasara wajen yaki da cutar a wasu wurare da kuma tsakanin wasu rukunoni, yayin da a wasu wurare na daban kuma, an bar annobar ta ci karenta babu babbaka, inda adadin mutanen da ta kashe ya yi ta karuwa.

A cewar wani rahoto da aka fitar, sabbin mutane miliyan 1.7 da suka kamu da cutar a shekarar 2019 sun ninka har sau 3, kan mizanin da aka sanya na rage sabbin masu kamuwa da cutar zuwa kasa da 500,000 a shekarar 2020.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*