?>

MDD: Isra'ila Ta Rushe Gidajen Palasdinawa Kusan 100 A Cikin Makwanni Biyu

MDD: Isra'ila Ta Rushe Gidajen Palasdinawa Kusan 100 A Cikin Makwanni Biyu

Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar hukumar mai kula da ayyukan agaji ta sanar da cewa; A cikin makwanni biyu kadai, Isra’ila (HKI) ta rusa gidajen Palasdinawa 90, ta kuma tarwatsa mutane 146 daga cikinsu, a cikin yankunan yammacin kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus.

ABNA24 : Rahoton da MDD ta fitar bayan makwanni biyu da yin hakan, ya bayyana cewa an yiwa Palasdinawa wannan ta’annatin ne a cikin wannan watan na Febrairu da muke ciki, a ranakun 3 da 8 ga watan.

Garuruwan da yahudawan sahayoniya su ka rusa gidajen dai, sun hada Humsa-al-Buqai’a, sai kuma kudancin al-Khalil da Umm al-Kheir da kuma Khirbet Tawamin.

Akwai kananan yara 83 wadanda lamarin ya shafa, kamar yadda rahoton ya ambata. Rusa gidajen Palasdinawa da mayar da su ‘yan gudun hijira wani abu ne da ya zama ruwan dare wanda yahudawan sahayoniya su ke yi a ko wace rana.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni