?>

Masu Bincike Na Burtaniya Sun Gano Wani Tsohon Masallaci A Iraki Da Aka Gina Karnin Farko Na Musulunci

Masu Bincike Na Burtaniya Sun Gano Wani Tsohon Masallaci A Iraki Da Aka Gina Karnin Farko Na Musulunci

A baya-bayan nan ne masu bincike na Burtaniya suka gano wani tsohon masallaci da wani wurin ibada a lardin Dhi Qar na kasar Iraki.

A baya-bayan nan ne masu bincike na Burtaniya suka gano wani tsohon masallaci da wani wurin ibada a lardin Dhi Qar na kasar Iraki, wanda yana daya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a cikin 'yan watannin nan a yankin.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a baya-bayan nan dai an gudanar da wasu muhimman ayyukan binciken kayan tarihi a lardin Dhi Qar na kasar Iraki, daya daga cikinsu shi ne wanda aka yi a fadar daya daga cikin sarakunan Babila, wanda aka gano a yammacin Nasiriyya babban birnin wannan lardin.

Haka kuma an samu wasu wukake da tukwane da turare da kayan aiki na wancan zamanin.

An gano wasu gine-gine a yankin, da suka hada da dakuna, da gidaje da masallaci a tsakiya.

An gina wannan masallaci a shekara ta 60 zuwa 80 bayan hijira wato zamanin Banu Umayya da aka gano a wannan yanki.

Haka kuma a arewacin lardin, an gano wani tsohon masallacin da aka gina tun zamanin farkon bayyanar musulunci, wanda shi ne karon farkon gini da masu binciken suka mafi muhimmanci a wurin.

Wuri na uku da wani masanin kayan tarihi dan kasar Burtaniya ya gano kwanan nan shi ne wurin bauta na Sumerian da aka gano a arewacin Nasiriyya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*