?>

Masallacin Fatima Zahra (AS) A Kasar Kuwait

masallacin Fatima Zahra (AS) a kasar Kuwait yana daya daga cikin fitattun masallatai na yankin yammacin Asia a halin yanzu.


ABNA24 : Bisa rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, masallacin Fatima Zahra (AS) a kasar Kuwait wanda ya shahara da snan Taj Mahal na Kuwait, a halin yanzu yana daya daga cikin fitattun masallatai na yankin yammacin Asia.

An fara ikin ginin wannan masallaci a cikin shekara ta 2008, an kuma kammala aikinsa a cikin shekara ta 2011, masallacin yana daukar masallata 4,000 a lokaci guda, kamar yadda kuma an yana hasumiya hudu masu tsawo mita 33.

An yi amfani da duwatsun marmar na kasar Iran wajen ginin wannan masallaci, kwarrarun injiniyoyin aikin gini daga kasashen Iran da India ne suka yi aikin gyara duwatsun da aka yi ginin masallacin da su, wanda aikin gyaran duwatsun ya dauke su tsawon watanni takwas.

Baya ga wurin salla, a masallacin akwai babban dakin taro na maza, da kuma wani dakin taro na mata, sai kuma babban wurin ajiye ababen hawa, wanda zai iya daukar motoci 1000 a lokaci guda.

342/

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni