?>

MANZON ALLAH YACE MU’UMINI BAI KASANCEWA MAI YAWAN TSINUWA ------- Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

MANZON ALLAH YACE MU’UMINI BAI KASANCEWA MAI YAWAN TSINUWA  ------- Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

ZAI YIWU MANZON ALLAH YA ZAMA MAI YAWAN TSINUWA BAYAN YA TABBATA CEWA MANZON ALLAH YACE MU’UMINI BAI KASANCEWA MAI YAWAN TSINUWA?

A karatun Al-Milal Wan Nihal wanda Sheikh Hamzah Muhammad Lawal ya gabatar a ranar Juma’a, 13/7/2018, a makarantarshi dake Kaduna ya bayyana cewa ba zai yiwu Manzon Allah ya zama mai yawan tsinuwa da zagi ba alhali ya tabbata an rawaito hadisi daga Annabi cewa  bai yiwuwa mumini ya kasance mai yawan tsinuwa.
Malam yace:
 “ AL-MU’UMINU MAN LA YAKUNU LA’AANAN, Mumini shine wanda bai kasancewa mai yawan la’ana, amma shi (Annabi) sun sanya shi LA’AANAN ko basu sanya shi ba? Dole ka fahimci cewa ya zama LA’AANAN (WAL IYAZU BILLAH), saboda sun ce yace ban da magani ya Allah in nayi ka mai da shi gafara da rahama. Mu’umin shine wanda bai kasancewa la’aaNan. AlMustadrak na AlHakim AnNisaboriy akan AsSahihaini.
“ Sannan fadinshi (sawa) ya inganta inda yake cewa, wannan yana cikin musallamat kowa ya inganta shi. Manzon Allah Yace zagin musulmi fasikanci ne- daga nan zaka fahimci ma’anar fasikanci- yakanshi kuma kafirci. AlBukhari da Muslim sun rawaito shi, AtTirmiziy ya rawaito, AnNisa’I ya rawaito, Ibn Majah ya rawaito shi, AtTabari, AlHakim AnNisaboriy, AdDaru Qutniy ya rawaito shi cewa zagin musulmi fasiqanci ne. Sannan fadinshi (sawa) ya inganta inda yake cewa “Ba tayar dani a matsayin mai yawan la’ana ba, an tayar dani ni kawai (shine WA INNAMA) don rahama. WAMA ARSALNAKA ILLA RAHMATAN… Ni ba a tayar da ni ba a matsayin mai yawan tsinuwa da la’ana. An tayar da ni ne kawai a matsayin rahama, sahihu Muslim, Muslim ya rawaito shi.
 “ Da fadinshi (sawa) ya inganta cewa, “Duk wanda ( akan sharadi, kowane ne wato, ba a dauke ma kowa hula ba, ba uzuri), duk wanda ya ambaci wani mutum- kowane mutum- da wani abinda yake babu shi a cikinshi (buhtan), to, Allah Ta’ala zai sashi a kurkuku a wutan Jahannama har sai ya zo da abinda zai goge wannan abinda ya fadi dangane da mutumin”. Subhanallah, daga ina zai zo dashi? To, yaya shi Manzon Allah (sawa) zai yi wannan? Wannan akwaishi a cikin Attargib, sannan akwaishi Addabarani ya rawaito shi da isnadi mai kyau (bi isnadin jayyid). Wa’yannan mutanen suna siffata wani Annabi wanda a wajensu ya inganta, koda ba a wurinmu ba inganta ba wannan abinda zan fadi yanzu. Yanzu wayannan mutanen haka suke siffata wani Annabi, wato wannan Annabin wanda yake a wurinsu fa ya inganta daga hadisin Muslim cewa wata rana Ummul Mu’umini A’ishah ta fusata, sai Manzon Allah (sawa) yace mata me ya same ki shaidaninki ya zo maki ne? Sai tace; to, kai baka da shaidan ne? Sai yace mata; Ina dashi mana- shi yasa muka ce ya inganta a wurinsu, muna so mu kafa hujja dashi ne. Ina da shaidan mana, saidai na roki Allah sai ya taimake ni akanshi, sai ya musulunta, saboda haka bai umurtata da komai sai alkhairi- ka ga shaidan ne amma yana umurtan Annabi da alheri.
 “To, akan wannan, hujja akansu ko? Cewa shaidaninshi ya musulunta, saboda haka baya umurtanshi da sharri. Shine suke siffata shi da wannan siffar cewa ya tsinema wani? shaidanin nashi bai umurce shi bane, bai hana shi ba? WAL IYAZU BILLAH, AYAZAN BILLAH, SUBHANALLAH. Basu yi Imani da Muslim din bane? Koko sun yi Imani da bangaren Muslim sun kafircewa bangaren muslim ne? Haka suke siffata wannan Annabin wanda yake a wurinsu ya inganta a Sahihu Muslim akan cewa yace shaidaninshi ya musulunta saboda haka bai umurtanshi sai alheri, to, ya aka yi ya zama cewa ya tsinema mutane ba tare da ya sani ba, ba tare da nufi ba? Saboda fusata saboda ila akhirihi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*