?>

MANZON ALLAH (SAWA) BAYA FUSHI DON DUNIYA ----- Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

MANZON ALLAH (SAWA) BAYA FUSHI DON DUNIYA  ----- Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

A karatun Al-Milal Wan Nihal wanda Sheikh Hamzah Muhammad Lawal yake gabatarwa domin bayanin aqidun shi’a na ranar juma’a, 28/6/2018, malamin ya bayyana Manzon Allah baya fushi domin duniya.

 A yayin da yake bayani dangane da matakin da wayanda basu ji dadin hukuncin da Manzon Allah (sawa) ya dauka ko yayi ba, ko a kansu, ko a kan wasunsu. Malamin yace wayannan mutane sun zo da hadisai domin su rusa wayancan matakan da Manzon Allah (sawa) ya dauka. Sannan yace a lokaci guda su wayannan mutane sun zo saboda su dauki fansa a kan shi Manzon Allah (sawa) din.
Malamin ya bayyana cewa irin wannan mataki da suka dauka shi ya sanya hadisai masu karo da juna suka yawaita a littafan Ahlus sunnah.
 “ A wani wuri su ce yana yin tasarrufi a cikin fushi, wani wuri kuma su ce yayi galaba a kan shedan ne saboda shedaninshi ya musulunta, sai kace tunda yayi galaba akan shedaninshi ya aka yi yake fushi akan nufi ba?
 “ Su da kansu sun rawaito cewa Manzon Allah (sawa) ya rantse da Allah akan cewa babu abinda yake fita daga bakinshi sai gaskiya, wannan kuma Allah Ya rigaye da fadi. To, sai muka ce; to, shi kaman yanda Amirul Mu’uminin Al-Imam Ali (as) ya siffata shi ne. Manzon Allah baya fushi don duniya- yana fushi watau, amma baya yi don duniya, don fizga ta rai ko ta ruhi, baya yi. LA YAGDIBU LID DUNYA….. To, amma idan gaskiya ta fusata shi, wato ya fusata don gaskiya- don duniya baya fushi- wato in hak ya taso. Idan gaskiya ta fusata shi,, IZAH AGDABAHUL HAQ, fa’il din shine ALHAQQU, wato ALHAQQU AGDABAHU, AGDABAHU HUWA ARRASUL. FA IZAH AGDABAHUL HAQQU, to, idan gaskiya ta fusata shi LAM YA’RIFHU AHADAN, ba wanda ke iya gane shi, inji Ali (as). Haka ya kamata mutum ya zama, koda ba zai iya zama ba ya kusanci haka. Ya zama yana tafiya ne akan asasin haq.
 “ Manzon Allah ba akan asasin haqq yake tafiya ba, shine haqq. Matakinshi shine haqq, kaman Allah Azza wa jal. Allah Yace QAULUHUL HAQQ, QAULU MAN? QAULULLAH, fadin Allah shine AlHaqqu. Fadin Manzon Allah shine AlHaqqu da izinin Allah Azza wa Jal. To, idan gaskiya ta fusata shi ba wanda ke gane kanshi, ba wanda zai iya tsaida shi sai yayi intisari ma gaskiya, ba alfarma ba tagomashi, ba ire iren wayannan, ba muyulaat na nafs kaman Allah Azza wa Jal. Muna cewa Allah shine AlMuntaqim ko? Daga cikin sunayen Allah akwai AlMuntaqim, HAL YANTAQIMU LI NAFSIHI? Allah yana daukan fansanshi dan kanshi? Irinmu in mutum ya fusata ka sai ka dauki fansa akanshi saboda thaura din fushi ta sauka. Haka Allah yake yi? Idan yayi fushi a cikinmu ya kan nemi ya dauki fansa saboda ya huce. Ruhin fansa shine ATTASHAFFI kaman yanda suke cewa, wato shine hucewa. To, shi Allah Subhanahu wa Ta’ala yak an dauki fansa ne saboda ya huce?
 “ Allah yak an dauki fansa ne saboda fansar kanta, saboda gaskiyar kanta. In kace menene amfani a gurin Allah? Saboda in muka dauki fansa amfanin shine wannan hucewar ko? To, shi Allah amfanin me yake samu? Amfanin yana a cikin fansar ne ita da kanta. Bari mu baka misali a nan wurin; zaka ga mutum yayi sata said an sanda ya kama shi sai a kai shi kotu sai a ce nan wurin akwai hakki guda biyu; akwai hakkin wanda barawon yayi ma sata, sannan akwai hakkin hukuma a cikin satan. Wani lokaci zaka ga mai hakki yace ya yafe amma sai hukuma tace bata yafe ba domin akwai hakkin hukuma, sai a ce THE STATE VS WANE, wato hukuma ta kai karan wane. To, mececen fa’idar da hukuman zata samu idan aka dauki fansa a kan barawon da ba ita yayi ma sata ba? Saboda kiyaye tsari, saboda fansar a kan kanta, saboda adalci. Ba wata fa’ida da take komawa ya zuwa gare ta ita. Wannan itace irin fansar Allah. Fansar Allah itace fansar hukuma ba irin fansar wanda aka zalunta aka yi ma laifi ba. Wanda aka yiwa laifi zai huce, in ya ga dama ya sayyarar da hakkinshi. Amma fansar hukuma ba irin wannan bace. To, haka Manzon Allah (sawa) yake.
 “ Manzon Allah (sawa) baya fushi baya fusata domin duniya- wannan Abadan- amma idan gaskiya ta fusantar dashi, yana fusata. Ai fusatan da Allah ya sanya a cikinmu akwai fa’idar ta, ba kowane fushi ne bai da kyau ba. Mutumin da sam sam bai fushi wannan bai da fadila. Ba fadila bane rashin fushi, shubha ce a mutane. Rashin fushi akan kanshi ba falala bace, a ina ka ajiye fushinka shine. Ya kanyi fushi sosan gaske amma ba da adifa ba, ba da fizga ta nafs ba, ta Allah Azza wa Jal.
 “ Kuma babu wani abu wanda yake tsayawa a gaban fushin Manzon Allah (sawa) har sai ya taimake ita gaskiya din. Shine kawai abinda ke tsaida shi. To, Kenan yanzu idan Manzon Allah (sawa) ya fusata sai ya tsine ma wani, akan haqq ne ko a kan badil? Shine nan suka ce yana yi akan badil (saraha). Manzon Allah yana fushi a kan badil ba akan haqq ba. Wani lokaci akan haqq, wani lokaci akan badil. To, menene bambamcin Manzon Allah da mu oho? Bamu gane ba. Ya aka yi ya zama Manzo mu ba manzanni ba? Suka ce Allah ne ya sashi ya zama Manzo akan dukkan nawaaqis dinshi. Amma duk da haka Allah yasa shi ya zama Manzo, haka suke so su ce. Manzon Allah kwata kwata bai yin abu akan kuskure. Manzon Allah bai yin abu akan ishtibahi. Manzon Allah bai yin irin wannan dama din, Manzon Allah bai yin nadama, bai yin da na sani irin namu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*