?>

DAWWANA HADISI A WAJEN MALAMAN SHI’A Zama na 3(3

DAWWANA HADISI A WAJEN MALAMAN SHI’A      Zama na 3(3

____Sheikh Hamzah Muhammad Lawal
…Cigaba

Ash-Sheikh Aghah Bazurg Dahraniy -Malamin Ash-Sheikhus Subhani-a cikin littafinshi “Az-Zari’ah Ila Tasanifish Shi’a” ya ambaci akalla kaman asali 130 daga cikin asulla 400,wato asulla da mawallafansu a matsyin misali.A juz’I na 2,shafi na 125 zuwa 167  a can wurin zaka gani.
Daga cikin 130 din -mu zamu ambaci kadan tayammunan saboda neman albarka.Daga cikinsu akwai Aslu Adam Ibn Husain Annuka Al-Kufiy As-Siqah,akwai Aslu Adam Ibn Mutawakkil Bayya’ul Lu’u lu’u Al-Kufiy As-Siqah -ka ga wannan yana sai da lu’u-lu’u,suna aiki,suna sana’o’i.Kaman daga cikin manya manyan malaman Ash’arawa akwai Ash-Sheikh Al-Baqillaniy,me yake saidawa?yana sai da gyada,Al-Baqilla shine gyada,sunan shi Al-Baqillaniy ko Al-Baqilla’iy.Wannan sunanshi “Bayya’ul lu’u-lu’u”amma kuma babban mutum a lokaci guda.Akwai dangantaka tsakanin saidawarka lu’u-lu’u da kamalolinka na addini da ilimi?
Akwai Aslu Abban Ibn Taglib Al-Kufiy As-Siqah,akwai Aslu Abban Ibn Usman Al-Ahmar Al-Bajaliy As-Siqah,akwai Aslu Abban Ibn Muhammad Al-Bajaliy As-Siqah,akwai Aslu Ibrahim Ibn Usman Ibn Ayyub Al-Kazzaz Al-Kufiy As-Siqah,halumma jarra,mu ba dole sai mun kawo duka wa’yanda ya kawo gabaki daya ba,don ka san wasu daga cikin sunayen su.
Wannan daga cikin marhala din Al-Majmu’atus Sagirah muka ce ko Al-Musannafatus Sagirah.To,bayan wa’yannan Al-Usul Al-Arba’u Ma’a din-sune asulla muka ce,sune maraja’,muka ce sune references-akwai “Al-Kutub Al-Ukhra” wato sauran littafan hadisi a wurin malaman shi’a.
Al-Kutub Al-Ukhra sune wasu littafai su kuma wa’yanda suke ba wadannan asulla dari hudu din ba wadanda su ma a zamanin A’immah (as) aka rubuta-ba wa’yannan Al-Kutubul Arba’a din ba,wato Al-Usul Kafiy ila akhirihi –sai dai cewa duk da yake a lokacin A’immah (as) aka rubuta su suma,ma’abutansu su basu lizamta ma kansu abinda mawallafan Al-Usul Al-Arba’u Ma’a suka lizamtawa kawukansu ba na qayyadantuwa da riwayar hadisi daga Imam kai tsaye ko kuma riwayar shi daga wanda yake rawaitowa daga shi Imam da wasida daya ba.
Zai yiwu wani lokaci su rawaito daga Imam kai tsaye,ko kuma su rawaito daga ma’abucin “asl” kai tsaye –ko lokacin Annabi a kan samu Sahabi yana rawaitowa daga Sahabbai daga Annabi,amma idan ka samu wanda kai tsaye ya rawaito daga Annabi din kuma aka ci sa’a ma ya rubuta a nan take da ya ji,shi wannan zinari ne ai,wannan jauhar ne,yana daga cikin jawaahir.
Zai iya rawaitowa daga ma’abucin “asl” kaman Abban Ibn Taglib kai tsaye,kuma zai iya rawaitowa daga gare su su biyu(wato Imam da ma’abucin “asl”) da wasida daya,wato ya rawaito daga wanda ya ji daga ma’abucin asl daga Imam.Ko ya rawaito daga Imam mubasharatan,ko ya rawaito daga ma’abucin asl,ko ya rawaito daga su biyun (wato Imam da ma’abucin asl) da wasida daya ko wasida “muta’addida”,wannan muna magana akan wanda bai shardanta ma kanshi abubuwan da ma’abucin asl ya shardantawa kanshi amma dukkansu sunyi zamani da Imam.Wannan baya nufin riwayoyinsu basu da kima amma kad’an basu kai kiman na ma’abuta Al-Usul Al-Arba’u Ma’a.
Zamu ambata saboda neman albarka –wato ba gaba daya zamu kawo ba,bamu son littafinmu ya zama cewa akalla ko da daya,biyu,uku babu daga cikin wa’yannan,manufarmu ba itace kawo gaba daya ba,manufarmu itace kawo wasu daga cikin su domin neman albarka.
Zamu ambaci wa’yannan anawinonin daga cikin majmu’an anawin din gabaki daya na wa’yanda Ash-Shaikhud Dahrani ya ambata,zamu dan ciro wasu mu sa littafi mu ma saboda neman albarka.
Daga cikin wannan gungun wanda sun yi zamani da A’immah (as) amma basu lizamta ma kansu abinda ma’abuta Al-Usul suka lizamta kawukansu ba.Akwai littafin hadis na Abu Yahaya Ibn Ibrahim Al-Bilad(Ibn Abil Bilad),akwai littafin hadisi na Ibrahim Ibn Abil Kiram Al-Ja’afariy,akwai littafin hadisi na Ibrahim Ibn Kalk Addar Al-Abidiy,akwai littafin hadisi na Ibrahim Ibn Saleh Al-Masiy Al-Asadiy da sauransu da sauransu,amma tayammunan mun ambaci kadan.
Yanzu muna da littafai da yawa na asali na zamanin farko a wannan marhalar ta Al-Majmu’atus Sagirah.
MARHALA TA BIYU :MARHALATUL MAJMU’ATIL KABIRA
Marhala ta biyu na yanda dawwana hadisinmu ya bi.Bayan an shude wannan  marhalar  ta farko,to,sai aka zo -a tarihin dawwana hadisinmu – marhala din littafai manya(Marhalatu Majmu’atil Kabirah).Wannan itace marhalar tanada da wallafa littafai manya manyan da a cikin aka tattara wadancan littafan na marhalan farko.
Wadancan Al-Masaadir din Al-Awwaliyyal Usul,sai ya zama yanzu an tattaro su gabaki daya an taskace su,duk abinda yake cikin can daya,biyu,uku,dari hudu,dari shida,yanzu sai wasu suka dora ma kansu tattara su a littafansu.
Nisba din kuskure a irin wannan tadwin din ta fi girma akan nisba din kuskure da zamu kwatanta ta da yanda aka rubuta littafai a wurin Ahlus-Sunnah Wal Jama’a duk da yake bamu yi magana akansu ba?ko ko nisba din kuskure zai zama cewa ta fi kadan?ta fi yawa ko tafi kadan?Me yasa?Har mutum yana da baki ya gaya mana cewa littafanmu basu inganta ba.Nisba din kuskure a littafanmu zai zama tafi kadan a littafanmu,duk da haka kuma akwai kuskure saboda su ba ma’asumai bane,akalla a marhala din gaba,wato bayan nan.Akwai kuskure amma nisba din kuskuren tafi zama kadan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*