?>

DAWWANA HADISI A WAJEN MALAMAN SHI’A Zama na 2(2)

DAWWANA HADISI A WAJEN MALAMAN SHI’A Zama na 2(2)

Na Sheikh Hamzah Muhammad Lawal
…Cigaba.

Saboda haka ya zama wa’yannan asullan guda dari hudu-na farko kenan-da kuma sauran littafai da mukai ishara ya zuwa gare su-wato daraja ta biyu din nan-dukkansu suna dogaro ne a matanoninsu na hadisi ya zuwa ga Imam (as).
Akwai Al-Usul Al-Arba’u ma’a din wa’yanda suka shardanta ma kansu wannan sharadin,su guda dari hudu.Sannan akwai saura wa’yanda su basu shardanta ma kansu wannan sharadin ba amma su ma suna a zamanin A’immah.Sai ya zama da wa’yancan dari hudun da sauran duka madda dinsu ta hadisi suna dogaro ne ya zuwa ga Imam (AS).Wato da dari hudun da wa’yanda basu din ba duka suna dogaro ne ya zuwa ga Imam (as).
Wa’yannan usul din guda dari hudu da kuma sauran littafan da muka yi ishara ya zuwa gare su suna tukewa ne zuwa ga Imam.Dukkan Imam din da ake rawaito wata riwaya daga gare shi a wannan marhala ta farko,shi kuma akan kanshi,wato ana shi bangaren,ita riwayar yana rawaito ta ne daga mahaifinshi,daga iyayenshi,daga Ali(as) a littafin da yai ishara ya zuwa gare shi wanda bamu fadi ba, shine “Kitabu Ali”,wanda shi kuma wannan Kitabu Ali din siffan shi shine “imla’in” Annabi(sawa) da “khaddin” Ali(as).Sune siffofinshi,wato Imla’in Manzon Allah da Khaddin Ali wanda a cikinshi akwai dukkan komai,har da diyyan yakushi.
Kenan,A’immah sun rawaito daga Ali (as),Manzon Allah (sawa) ya karba daga Jibra’il(as) daga Allah Azza wa Jal.Ali (as) ya karba daga Manzon Allah (sawa),A’immah sun amsa daga Ali(as),malaman shi’a sun amsa –a wannan marhalan- daga A’immah(as).An fahimci wannan surar?Surar ta kawwanu?
Dukkan Imam din da ake rawaitowa daga gare shi,shi kuma a nashi bangaren yana rawaitowa daga mahaifinshi,daga iyayenshi,daga littafin Ali(as).Kenan,hadisan A’immah “musnada” ne?ko “munkadi’a”  kuma “mursala”?Wannan zai warware maka matsalar da shubhar da ake fadi cewa babban mishkilar hadisan shi’a itace rashin isnad.Wannan shubha ce ko ishkal?Sunanta shubha.
Sannan kuma yana magana a marhalan da ta zo bayan wannan marhalan wadda ita din tana dangantaka da wannan marhalan wadda zata bayyanawa mutum idan muka zo a nan gaba insha Allah.Babu hadisan da suka fi hadisan shi’a zama musnada a wannan marhalan.Malaman mu a wannan marhalan sun rawaito kai tsaye daga A’immah (as) ko da wasa’id,su kuma A’immah sun rawaito daga iyayensu,daga Ali(as),daga Manzon Allah(sawa),daga Jabra’il (as),daga Allah Azza wa Jal.To,kuma daga Imam,wato isnadin wa’yannan riwayoyin daga Imam –kowanne Imam-din (ba daga wa’yanda suka rawaito daga Imam din ba) har zuwa Allah Azza wa Jal shine wannan isnadin wanda aka sanshi a cikin urfin malaman hadisi –wato “al-urful khas”- na sunnah da shi’a da isnadi na zinari(wato Silsilatuz zahab),wato Malaman shi’a da sunna.Wannan isnadin da muka ambata yanzu daga Imam zuwa Allah Subhanahu wa Ta’ala ba yankewa shine malaman hadisi na shi’a da sunnah suke kira da “silsilatuz zahab”,wato daga Imam daga mahaifinshi daga kakanshi daga kakan-kakanshi zuwa Ali(as) zuwa Manzon Allah zuwa Jabra’il zuwa Allah Azza wa Jal.Malaman hadisi duka sun sani,ba kowa mutum muke nufi ba.
Me yasa suke mashi “silsilatuz zahab”?Saboda tsabtan wannan isnadin.-dukkansu ma’asumoon,dukkansu bayin Allah,dukkansu kammalallu,ba yankewa sam- da kasantuwanshi fes,da kuma daukakan kiman shi wato ita riwayar,wato ba zai samu shakka ba.Wannan isnadin wanda yake dumaninantar da mutum,wanda yake kwantarwa mutum hankali,wanda yake gamsar da mutum yasa ya natsu.
Shine isnadin da malaman sunnah suke cewa idan aka karantawa mahaukaci zai warke,shine wanda malaman sunnah suke cewa idan mutum ya karantawa mara lafiya da niyyar shifa,da niyyar warkewa zai bar’anta,zai warke.

A-Usulul Arba’u Ma’a

Wannan asullan guda dari hudu;sune littafai – kowanne sunan shi asl daga cikinsu- guda daddai har guda dari hudu,kowanne daga cikinsu an sa mashi suna “asl”,da ma’anar makoma,wato sune references a ta’abiri na yau,wato maraja’,wato masaadir.Kowanne daya sunanshi marja’a ko masdar,da ma’anar reference.
Me yasa aka sanya mashi wannan sunan?Saboda komawan malamai ya zuwa ga wa’yannan littafan da dogaronsu akan littafan,saboda daga A’immah ne riwayoyin kai tsaye muka ce.Saboda haka sune littafai na farko madogara,sune madogara ta farko.Kana iya kiyasin adadin hadisan da suke ciki.Malamai dari hudu ne kowa ya rawaito nashi daga Imam din da ya rawaito ko Imaman.
Wa’yannan littafan sun kebanta da wasu ababen da suka kebanta dasu a wurin malamai na wasu siffofi na daban na musamman,wato Al-Usul Al-Arba’u Ma’a.Daga cikin wa’yannan khususiyoyin akwai:
Na farko,sun fita daban wa’yannan asullan –ku saurara sosai ku ji littafanmu ta ina muka samo su,ba wa’yancan usul din ba wa’yanda suke a hannayen mu,daga ina suka zo?Sun fita daban da manhajinsu na musamman.Meye manhajin?manhajinsu na yanda aka wallafa su wanda na yi ishara ya zuwa gare shi datsun nan.
Wanne ne wannan manhajin?Wanda shine cewa hadisin da aka rubuta a cikinsu,a cikin wa’yannan Usul din dari hudu,ko ya zama an rubuta hadisin ne da riwayar shi mawallafin littafin daga Imam kai tsaye,ko kuwa ta hanyar riwayar shi mawallafin wadda ya rawaito daga wanda ya rawaito daga Imam mubasharatan.Wato ko shi da kanshi –wannan itace mizah ta farko-ko kuma daga wani daga Imam.
Na biyu -daga cikin mizozi na wa’yannan Al-Usul Al-Arba’u Ma’a din,wanda ba mutanen da suke da littafin hadisi wanda yake da wannan kimar.Shine yabo da aka yi wa wadanda suka wallafa su daga wurin malamai wa’yanda suka san kimar hadisi,wato yabo na musamman wanda ya gangaro akan wa’yannan asullan wanda wannan yabon ya wajabtar da ayi I’itiqadi a ce abinda ke cikinsu ya inganta(ingantacce ne),yabon da ya zo daga wurin malaman mu na farko.
Ash-Sheikh  Agha Bazurg Ad-Dahrani daga cikin manya manyan malaman hadisai daga cikin malaman Ayatullah Ja’afar Subhani da manya manyan Ayoyinmu na yanzu da kuma na da.Ayatullahi Agha Bazurg Ad-Dahrani a cikin littafinshi Azzari’ah Ila Ta’alifish Shi’a,wato tsani ya zuwa ga littafan shi’a.
An yi ma shi’a gori ne cewa basu da littafai ba.Wasu wa’yanda basu sani ba daga malaman sunnah –irin wannan abinda kake ji ana fadi a nan da can  cewa ‘yan shi’a basu da littafai.To shine ya daukan ma kanshi zuwa library library ,dakunan ajiye littafan duniya gabaki daya domin ya rubuta fihris kawai na littafan shi’a.Ya rubuta adadin littafan shi’a wa’yanda kokarinshi ya kai ga zuwa gare su muke so muce.Sa’ayin mutum nawa ne?mutum daya kawai,shine Ash-Sheikh Agha Bazurg Ad-Daharani ya zo da mujalladai na ban mamaki na sunayen littafai kawai da ta’alikoki da sharhohi na “muhtawayaat” dinsu da sauransu.
A wannan littafin,Azzari’ah Ila Ta’alish Shi’ah, juz’I na biyu,shafi na 126 zuwa 132,yake cewa:
  “Ash-Shaikhul Baha’iy ya rubuta a wannan littafin na shi,ya ambaci al’amuran da suke wajabta,da suka sanya malaman mu na da suke iya yin hukunci da ingancin hadisi.Sharudda da suke sanya su suce wannan hadisin ya inganta,wato malaman da.Daga cikinsu sai ya kirga da cewa shine samuwan hadisin a cikin da yawa daga cikin wa’yannan asullan guda dari hudu sanannu shararru wadanda suke kekkeyayawa a tsakaninsu.”
Wato mujarradin an samu hadisin a cikin wannan usul din na Al-Arba’u Ma’a,wannan yana daya daga cikin dalilin da suke cewa hadisi ya inganta.Wato kasantuwan hadisin a cikin asl din shi kan kanshi dalili ne akan ingancin shi hadisin.Me yasa ?Saboda wa’yancan abubuwan guda biyu da muka fada maka a asali.Balle kuma a same shi asl daya,asl biyu,asl uku,a asulla da yawa,me yake nufi kenan?Sai ya cigaba da cewa:
  “…daga cikin abubuwan da suke inganta hadisi a wurin malaman mu na da shine maimaituwan hadisin.In hadisi ya maimaitu a asali ko asali guda biyu daga cikin wa’yannan asulla din da isnadai daban daban masu yawa(ba isnadi daya ba)”
Na farko afku a asl daya,asl biyu,asl uku ko fiye da haka.Na biyu kuma da isnadi masu yawa,isnadoji daban daban mukhtalifa,sai suce mashi wane irin hadisi?288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*