Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo labarin cewa, an gudanar da taron majalisar malamai ta mabiya mazhabar shi'a na kasar Pakistan a birnin Karachi na ranar tunawa da rushe Baqiya. Sayed Asad Iqbal Zaidi shugaban majalisar malamai na kasar Pakistan a lardin Sindh ne ya yi jawabi a wajen taron.