?>

Libiya : Saif al-Islam, Zai Tsayawa Takara A Zaben Shugaban Kasa

Libiya : Saif al-Islam, Zai Tsayawa Takara A Zaben Shugaban Kasa

Dan tsohon shugaban kasar Libya mirigayi Muammar Gaddafi, cewa da Saif al-Islam, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar.

ABNA24 : Saif al-Islam, ya bayyana haka ne wata hira da jaridar ‘New York Times’ a garin Zintan, dake yammacin kasar.

ya ce a cikin shekaru 10 da suka gabata, babu abin da ‘yan siyasa suka tabaka wa kasar face tashin hankali, yana mai cewa lokaci ya yi da za a koma yadda ake a da.

Dan shekaru 49, Saif al-Islam, shi ne akayi ta kallon zai gaji mahaifinsa Muammar Gaddafi, wanda aka kashe a cikin shekarar 2011, yayin boren neman sauyin da ya barke a kasar.

An dai shafe shekaru ba’a ji duriyar Saif al-Islam ba, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa jallo.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*