?>

Lebanon: Kotu Ta Hana Gwamnan Babban Bankin Kasar Fita Daga Kasar

Lebanon: Kotu Ta Hana Gwamnan Babban Bankin Kasar Fita Daga Kasar

Wata kotu a kasar Lebanon ta fidda sammacin hana gwamnan babban bankin kasar fita daga kasar saboda zarginsa da cin hanci da rashawa da almundaha da kudaden jama’a.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Haitham Ezzo wani lauyan masu gabatar da kara ya fadawa tashar talabijin ta Aljazeera kan cewa ana tuhumar Riad Salameh wanda yake shugabancin babban bankin kasar kusan shekaru 30 da suka gabata, kan al-amura da suka shafi cin hanci da rashawa da arzuta kansa da dukiyoyin al-umma da kuma almundahana.

Amma gwamnan ya sha musanta cewa yayi ba daidai ba a matsayinsa na gwamnan babban bankin kasar.

Mai sharia Ghada Aun ya bayyana cewa bisa shaidun da suka shiga hannunshi za’a yiwa gwamnan babban bankin kasar tambayoyi a gobe Alhamis, don tabbatar da wasu bayanai masu muhimmanci wadanda suka shiga hannu.

Kafin haka dai an yiwa wasu ma’aikatan babban bankin kasar tambayoyi kan ayyukansu a bankin.

Kasar Lebanon dai ta fada cikin matsalolin tattalin arziki mafi tsanani a tarihin kasar a cikin shekaru biyu da suka gabata, saboda aikata ba dai dai ba wanda wasu jami’an gwamnatin kasar suka yi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*