?>

Lebanon: Jubran Basil Ya Ce Babu Gwamnati Mutakar Shugaban Kasa Bai Amince Ba

Lebanon: Jubran Basil Ya Ce Babu Gwamnati Mutakar Shugaban Kasa Bai Amince Ba

Shugaban jam’iyyar “National Free Movemrnt” wacce kuma take cikin gamayyar jami’yyun kasar da ake kira “Lobanon Mai Karfi” Jubron Bsil ya bayyana cewa ba zai yu a kafa gwamnati a kasar ba, sai tare da amincewar shugaban kasa Michel Aun.

ABNA24 : Jaridar Anashra ta kasar Lebanon ta nakalto Basil yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kowa yana son a kafa gwamnati da gaggawa, amma wannan alhakin ya rataya ne kan wuyoyin firai ministan da aka nada, Sa’adul Hariri da kuma shugaban kasa Michek Aun.

Basil ya kara da cewa su ne wadanda yakamata su warware matsalolin da suka hana gwamnatin kafuwa, wadanda suka hada da yadda gwamnatin za ta kasance, yawan ministoci da kuma rabon ma’aikatu tsakanin ministocin.

Basil ya kara da cewa dole en Sa’adul Hariri ya amince kan cewa gabatar da gyara a kundin tsarin mulkin kasar na majalisar dokoki ne, a yayinda kafa gwamnati kuma na bangaren zartarwa.

Tun cikin watan Octoman shekarar da ta gabata ce aka bawa Saadul Hariri damar kafa gwamnati, amma ya kasa yin hakan saboda sabani tsakaninsa da shugaban kasar kan wasu al-amura .

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni