Za'a fara aikin ginin Masallaci na farko da izinin Gwamnatin Girka a Athens

Za'a fara aikin ginin Masallaci na farko da izinin Gwamnatin Girka a Athens

Bayan kwashe shekaru 17 ana jinkirta ginin Masallaci a birnin Athen na kasar Girka, a yanzu haka dai ta tabbata cewa za’a fara aikin ginin masallacin na farko da izinin Gwamnati a irnin Athens.

Sai dai kuma wasu musulmi na cewa sai sun ga an kammala ginin ne za su yi hamdala.

Wannan gari na Athens na da musulmi akalla dubu 300.

Ana ganin kara yawan musulmi ‘yan gudun hijira daga kasashen Afghanistan, Pakistan da Masar, ya sa ake ganin mahukuntan kasar ke bada amincewarsu domin a samarda masallaci na farko da Hukumomi suka amince da shi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky