'Yan sandan Spain sun kame manyan jami'an gwamnatin yankin Catalonia

'Yan sandan Spain sun kame manyan jami'an gwamnatin yankin Catalonia

‘Yan sandan kasar Spain sun kame wasu manyan jami’an gwamnatin yankin Catalonia na kasar Spain, a wani samame da suka kai ofisoshinsu da safiyar yau Laraba. Matakin dai shi ne irinsa na farko da gwamnatin Spain ta dauka kan yankin na Catalonia, a kokarinta na dakile yunkurinsa na kada kuri’ar rabar gardamar ballewa daga kasar.

Tuni dai zaman zulumin da ake a yankin na Catalonia ya karu domin kuwa cikin manyan jami’an gwamnatin da aka kama har da karamin ministan tattalin arzikin yankin Josep Maria Jove, kamen da Shugaban yankin na Catalonia Carles Puigdemont ya zargi gwamnatin Spain da kokarin musgana musu kan ‘hakkin samun yancin da su ke nema, ta hanyar kakaba musu dokar ta baci baya ga kame masa manyan jami’an.

Sai dai Firaministan kasar Spain Mariano Rajoy ya kare umarnin da suka bada da cewa tilas suka dauki tsattsauran matakin saboda bijirewa umarnin kotun kolin kasar da shugabannin yankin na Catalonia ke yi, na dakatar da shirinsu na kada kuri’ar raba gardamar neman ballewar yankin daga spain a anar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

Manyan ma’aikatun da ‘yan sandan spain suka kaiwa Samame a Barcelona sun hada da Mai’aikatar lura da tattalin arzikin yankin wadda aka damke ministan ta, maikatar harkokin kasashen ketare, sadarwa, da kuma ofisoshin da ke da alaka da na shugaban yankin na Catalonia wato Carles Puigdemont.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni