Shugaban Rasha Ya Jaddada Cewa Kasarsa Bata Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Siriya

Shugaban Rasha Ya Jaddada Cewa Kasarsa Bata Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Siriya

Shugaban Rasha ya jaddada cewa: Kasarsa bata tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Siriya iyaka dai tana taimaka mata a fagen yaki da ta'addanci.

Gidan talabijin na Al-Mayadeen ya watsa labarin cewa: Shugaban Rasha Viladimir Putin ya jaddada cewa; Kasarsa bata tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Siriya, iyaka dai tana gudanar da ayyukan da kasashen biyu suka cimma yarjejeniya a kai na yaki da 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a cikin kasar.

Putin ya kara da cewa: Aikin rundunar sojin Rasha a cikin kasar Siriya shi ne murkushe 'yan ta'adda tare da kokarin ganin halattacciyar gwamnatin kasar ta ci gaba da shimfida ikonta a duk fadin kasar ta Siriya.

Har ila yau shugaban kasar Rasha ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun yake-yake a tsakanin wasu bangarori da suke da sabanin akida a kasar ta Siriya; Yana mai bayyana hakan da cewa; Babbar barazana ce ga hadin kan kasar. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky