Shugaban Kasar Turkiyya Ya Ce: Kungiyar NATO Tana Taimakon 'Yan Ta'addan Da'ish

Shugaban Kasar Turkiyya Ya Ce: Kungiyar NATO Tana Taimakon 'Yan Ta'addan Da'ish

Shugaban kasar Turkiyya ya yi furuci da cewa: Wata kasa daga cikin kungiyar tsaro ta NATO ta taka gagarumar rawa a fagen mallaka wa kungiyar ta'addanci ta Da'ish makamai a kasashen Iraki da Siriya

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan bai fito fili ya fayyace sunan kasar da ta taka gagarumar rawa a fagen mallaka makamai ga kungiyar ta'addanci ta Da'ish mai kafirta musulmi a kasashen Iraki da Siriya ba, kawai ya takaita ne da bayyana yadda wasu kasashen yammacin Turai suke da hannu dumu-dumu a kokarin wargaza wasu kasashe masu cikakken yanci kai a yankin gabas ta tsakiya domin cimma wasu munanan manufofinsu ta siyasa.

Hakika babu shakka kan wannan furuci na shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan cewa: Wata kasa daga cikin kungiyar tsaro ta NATO ta taka gagarumar rawa a fagen mallaka wa kungiyar ta'addanci ta Da'ish makamai, kuma tuni wannan lamari ya fito fili tun a lokacin yakin neman zaben shugabancin kasar Amurka tsakanin Hillary Clinton da Donald Trump.

Hillary Clinto tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka ta yi furuci da cewa: Gwamnatin Amurka ce ta kafa kungiyar ta'addanci ta Da'ish da nufin rusa kima da mutuncin addinin Musulunci a idon duniya tare da cimma manufofinta na siyasa a yankin gabas ta tsakiya, inda wannan furuci na Hillary Clinton ya kara fayyace bakar siyasar munafuncin Amurka a idon duniya musamman a yankin gabas ta tsakiya.

A fili yake cewa: Batun mallaka wa kungiyoyin 'yan ta'adda da suke yaki a kasashen Iraki da Siriya makamai da kudade lamari ne da yake sananne a tsakanin masu bincike, masana da manazarta gami da 'yan jaridu, misali kan haka shi ne; rahoton da Dilyana Gaytandzhieva 'yar jaridar kasar Bulgaria ta wallafa cewa: Daga cikin ayyukan munafuncin kasar Amurka, Haramtacciyar kasar Isra'ila, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa shi ne aikewa da muggan makamai da kudade ga kungiyoyin 'yan ta'adda na Da'ish da Al-Qa'ida karkashin jagorancin Hukumar Leken Asirin Amurka ta CIA da kungiyar tsaro ta NATO.

Har ila yau rahoton Madam Dilyana ya fayyace cewa: Wasu jiragen sama da suke jigila a duniya da sunan gudanar da huddan jakadanci sun kutsa sassa daban daban na duniya dauke da makamai suna mallaka wa kungiyoyin 'yan tawaye da na ta'addanci, kuma jirgin saman gwamnatin Jamhuriyar Azerbaijan yana daga cikin wadannan da suka taka gagarumar rawa a wannan fage. Bayan wallafa wannan rahoto, mahukuntan kasar Bulgaria sun dauki matakin korar Madam Dilyana Gaytandzhieva daga aiki.

A gefe guda kuma ita kanta gwamnatin Turkiyya karkashin jagorancin Rajab Tayyib Erdogan ta yi kaurin suna a tsakanin kasashen da suke tallafa wa kungiyar ta'addanci ta Da'ish a kasashen Siriya da Iraki, saboda haka kamar yadda shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya fito fili ya tona asirin cewa: Wata kasa daga cikin kasashen kungiyar tsaro ta NATO ta taka gagarumar rawa a fagen mallaka wa kungiyar ta'addanci ta Da'ish makamai, haka mahukuntan kasashen Iraki da Siriya suka bayyana cewa: Gwamnatin Turkiyya tana da hannu dumu-dumu a aiwatar da kisan gilla kan al'ummun kasashensu sakamakon tallafawa kasar Amurka da wasu kasashen yammacin Turai gami da 'yan koransu na kasashen Larabawa musamman Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa wajen jigilar 'yan ta'adda da makamai zuwa kasashen Siriya da Iraki.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni