Sabon Shugaban Kasar Faransa Ya Shiga Fadar Elysee

Sabon Shugaban Kasar Faransa Ya Shiga Fadar Elysee

Sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya shiga fadar Elysee da ke birnin Paris, inda ya yi rantsuwar kama shugabancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi rantsuwar kama aiki a matsayinsa na zababben shugaban kasar.

Shugaban Faransa mai barin gado Francois Hollande ya zagaya da Macron a cikin fadar Elysee, ya kuma yi bankwana da shi da kuma dukkanin ma'aikatan wurin.

Macron dan shekaru 39, shi ne shugaban kasar Faransa na farko mafi karancin shekaru, ya kum ayi alkawalin ci gaba da gudanar da ayyukansa domin ci gaban kasarsa da al'ummarsa da kuma nahiyar turai.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni