Paris: ‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga

Paris: ‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga

Hukumar ‘Yan Sandan Faransa ta ce jami’anta guda biyu sun jikkata lokacin da aka samu arangama tsakaninsu da matasan da ke zanga-zangar ranar ma’aikatan kwadago da ke zuwa kwanaki 6 a gudanar da zaben shugaban kasar.

Rahotanni sun ce, matasan da suka rufe fuskokinsu sun yi ta jifar ‘Yan Sanda wadanda suka mayar da martani da hayaki mai sa hawaye.

‘Yan sandan kuma sun yi amfani da harsasan roba domin tarwatsa masu zanga-zangar sama da 200.

Zana zangar dai ta samo asali ne daga jerin gwanon al’ada na kungiyoyin kwadago da ake gudanarwa 1 ga Mayu duk shekara.

Masu zanga-zangar a Paris sun fito rike da da kyallayen da ke dauke da sakwannin rashin jin dadi kan koma bayan ci gaban rayuwa mai inganci a kasar, da kuma nuna kyama ga jam’iyar masu tsatsauran ra’ayi ta Marine Le Pen da ke shirin fafatawa da Emmanuel Macron dan takara mai zaman kansa a ranar 7 ga Mayu

Za a iya cewa dai kanun kungiyoyin kwadagon da suka gudanar da jerin gwanon na yau litanin sun rabu dangane da kiran kauracewa zaben Marine Le Pen

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni