Mutane sun mutu a harin ta'addancin da aka kai a Burtaniya

Mutane sun mutu a harin ta'addancin da aka kai a Burtaniya

Rundunar 'yan sandan Burtaniya ta ce mutum hudu ne suka mutu, cikin su har da dan sanda da kuma wani mahari a harin da aka kai a ginin majalisar dokokin kasar.

Wata mata da ke tafiya a kasa na cikin mutanen da mota ta kade a kan gadar Westminster.

Haka kuma an caka wa wani dan sanda wuka a majalisar dokokin ta Burtaniya da ke tsakiyar birnin London, koda yake an harbe maharin da ya caka masa wukar.

Akalla mutum 20 ne suka jikkata, cikin su har da 'yan sanda uku.

Firai Ministar kasar Theresa May za ta gudanar da taro kan tsaron kasar nan gaba kadan.

Hukumar tsaron ruwan birnin London ta ce an ceto wata mata daga kogin Thames, kuma ana ba ta kulawar gaggawa.

Firai Ministan Faransa Bernard Cazeneuve ya ce daliban kasar uku na cikin wadanda suka ji rauni sannan ya aike da sakon jaje da goyon baya ga Burtaniya.

Shugaban majalisar wakilai David Lidington ya shaida wa 'yan majalisar cewa "'yan sanda dauke da makamai sun harbe mutumin da ake zargi da kai harin".

'Yan majalisar sun ce sun ji harbin bindiga sau uku zuwa hudu. Wata majiya a fadar Firai Ministar Burtaniya ta ce babu abin da ya samu ita Firai Ministar Theresa May.

An ga lokacin da ake shigar da Theresa May ckin wata mota samfurin Jaguar a lokacin da ake harbe-harbe a cikin majalisar dokokin.

Wani ganau, Radoslaw Sikorski, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Twitter wanda ya nuna mutanen da suka ji rauni kwance a kan titin Westminster Bridge.

Ya ce: "Yanzu wata mota ta kade mutum biyar."

Rundunar 'yan sandan kasar ta ce an kira ta domin magance harin da aka kai da makamai a kan gadar Westminster a yayin da aka raunata mutane da dama.

An dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta hanyar karkashin kasa da ke bi ta Westminster, sannan aka sauya wa motocin bas hanya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky