Mahara sun hallaka mutane 7 a birnin London

Mahara sun hallaka mutane 7 a birnin London

Wasu mahara sun halaka mutane 6 tare da raunata wasu 48, bayanda sukai amfani da wata mota, wajen bi takan masu tafiya a kasa, a kan gadar birnin London, kafin daga bisani maharan, su kutsa kai, cikin kasuwar Borough da ke kusa, inda suka aukawa duk wanda suka tarar, sara da wuka.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin, Mark Rowley, ya ce, jami’ansu, sun samu nasarar halaka maharan guda uku, wadanda suka ce, suna rataye da damarar abubuwan fashewa, sai dai bayan da aka bincika, sun gano cewar na bogi ne.

Harin na daren jiya Asabar, ya zo ne, bayan wanda a kasa da makwanni biyu, aka kai wani a birnin Manchester, wurin taron waka, inda wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 22.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. Wanda tuni magajin birnin London SadiqKhan da Fira Ministea Theresa May sukai Ala wadai da shi.

Wani lokaci a yau lahadi Fira minista May zata jagoranci wani taron gaugawa na majalisar tsaron kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni