Kungiyar Da'esh Ta Dau Alhakin Kai Harin Las Vegas

Kungiyar Da'esh Ta Dau Alhakin Kai Harin Las Vegas

Kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ko (IS) ta dau alhakin harin bindiga da kawo yanzu ya hallaka mutane 58 a wani wajen rawa a birnin Las Vegas na Amurka.

A sanarwar data fitar ta shafin yada farfagandanta na (Amaq), kungiyar ta ce dan bindigan mai suna Stephen Craig Paddock ya musulinta ne a 'yan watannin baya baya nan.

Kungiyar ta ce maharin ya karbi kiran ta ne na daukan fansa akan kai hare-hare ga kasashen dake cikin kawancen kasa da kasa da Amurka ke jagoranta wajen yakarta.

Shi dai ba'amurken dan shekaru 64 a duniya ya hallaka mutane sama da hamsin tare da raunana wasu daririwa a ruwan harsashen da ya yi tun daga hawa na 32 na benen wani otel mai suna, Mandalay Bay Hotel, kan wani dandazon jama'a dake halartar wani filin raye-raye na bainar jama'a.

Tun da farko dai bayanai sun ce 'yan sanda sun kashe mutimin, saidai rahotanni baya bayan nan sun ce mutimin ya hallaka kansa ne kafin 'yan sanda su tarda shi.

Wannan dai shi ne harin bindiga mafi muni da aka taba gani a Amurka.

Shugaba Donalt Trump a wani jawabinsa da yammacin nan ya danganta harin da babban abun takaici.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni