Hollande ya goyi bayan Macron

Hollande ya goyi bayan Macron

Shugaban Faransa Francois Hollande ya sanar da matakin marawa Emmanuel Macron baya a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 7 ga Mayu, tare da bayyana hadarin da ke tattare da zaben Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayin rikau.

Hollande ya ce Macron zai kada wa kuri’arsa tare da bayyana cewa zaben Le Pen barazana ne ga makomar Faransa a Tarayyar Turai.

Macron dai ya taba rike mukamin Ministan tattalin arziki a gwamnan Hollande, amma a watan Agusta ya fice gwamnatin.

Wannan ne karon farko da Macron ya tsaya takara a siyasar Faransa wanda ya kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa cikin watanni 12.

Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a na ci gaba da tabbatar da cewa Macron ne zai lashe zaben a zagaye na biyu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky